Shugabannin bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan na kasar Sin sun gana da junansu
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban hukumar yankin Taiwan na kasar Sin a wani babban Otel na kasar Singapore da yammacin ranar Asabar 7 ga wata. A yayin ganawar, shugabannin bangarorin biyu sun sha hannu sosai, matakin da ya bude sabon shafi na dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, wanda kuma zai zama wani muhimmin lokaci a tarihi. (Amina)