Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wasu wakilan kasashen waje da suka halarci taron kasa da kasa karo na biyu, kan batun fahimtar kasar Sin a ranar Talatar nan a birnin Beijing.
Yayin ganawar tasu, Mista Xi ya bayyana ra'ayinsa kan makomar tsarin yin kwaskwarima a gida, da bude kofa ga kasashen waje da Sin ke kai, da tsarin zirin daya da hanya daya, da taron koli na G20 da Sin za ta karbi bakunci a shekarar 2016 da dai sauran muhimman batutuwa.
Xi ya kuma jaddada cewa, Sinawa na kokarin farfadowa al'ummarsu, kana hakikannin shaidu sun nuna cewa, hanyar da Sin take bi ta gurguzu mai tsari tana dacewa da halin da Sin ke ciki. Hakan a cewarsa, ya sa Sin ci gaba da nacewa ga hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da sa kaimi ga kafa sabuwar dangantaka ta mutunta juna da samun moriyar juna, da kuma nacewa ga yin zaman tare tsakanin kasa da kasa.
Haka zalika, Mista Xi ya jinjinawa gudummawar da wakilan kasashen waje suke bayarwa game da sa kaimi ga mu'ammala tsakanin kasashensu da kasar Sin. A cewarsa, mu'ammala mai zurfi tsakanin jama'ar kasa da kasa na da muhimmanci kwarai da gaske. (Amina)