Shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan sun tashi da safiyar yau Alhamis daga nan birnin Beijing don ziyarar aiki a kasashen Vietnam da Singapore.
Shugaba Xi wanda shi ne babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC zai fara da ziyarar kasar Vietnam ne daga yau Alhamis 5 ga wata zuwa gobe Jumma'a 6 ga wata bisa gayyatar da takwaransa babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis na kasar Vietnam Nguyen Phu Trong da shugaban kasar Truong Tan Sang suka yi masa.
Bayan ziyarar a kasar Vietnam, shugaba Xi zai tashi zuwa kasar Singapore daga gobe Jumma'a 6 ga wata zuwa Asabar 7 ga wata, shi ma bisa gayyatar shugaban kasar Tony Tan Keng Yam.(Fatimah)