A ranar Alhamis din nan shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana ta shafin jaridar Nhan Dan ta kasar Vietnam cewar, idan kasashen Sin da Vietnam suka hada hannu don yin aiki tare, za'a samu kyakkyawar makoma a nan gaba.
Kasashen biyu, na makwabtaka da juna ta gabar teku da kuma tsaunuka, kuma sun shafe shekaru da dama da kulla dangantaka a tsakanin su.
Jaridar ta rawaito Mista Xi kuma sakatare janar na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na bayyana wannan manufa ne a birnin Hanoi, yayin ziyararsa ta farko a kasar ta Vietnam don amsa goron gayyatar da sakatare janar na jam'iyyar kwaminis na kasar Nguyen Phu Trong, da shugaban kasar Truong Tan Sang suka yi masa.
Kasashen biyu, sun jima suna yin mu'amala tare da juna, musamman wajen gina kyakkayawar alaka dake tsakanin su, wanda ke samar da alfanu ga kasashen biyu.
Kasar Sin ta kasance babbar aminiya ga Vietnam ta fuskar huldar kasuwanci sama da shekaru 11 da suka gabata, kuma Vietnam ta kasance kasa ta biyu mafi girma a kudancin Asiya da kasar Sin ke yin mu'amala da ita, sannan ana sa ran kasuwancin dake tsakanin kasashen biyu zai kai dalar Amurka biliyan 100 a nan gaba.(Ahmad Fagam)