Yau Litinin 26 ga wata ne, a birnin Paris, hedkwatar kasar Faransa, aka bude taron dandalin tattaunawa a tsakanin matasa karo na 9, wanda hukumar ilmi, kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO ta shirya, inda kuma shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aika da sakon murnar bude taron a madadin gwamnatin Sin da jama'arta.
A cikin sakonsa, shugaba Xi ya jaddada cewa, makomar kowace kasa ta rataya ga matasa. Muddin matasan duniya suka cika burinsu, sannan suka sauke nauyinsu yadda ya kamata, to, 'yan Adam za su fuskanci makoma mai kyau, kuma za a ci gaba da kara kokarin kiyaye zaman lafiya da samun ci gaba ba tare da kasala ba.
Ana sa ran matasa daga sassa daban-daban na duniya za su girmama juna, su yi koyi da juna, su kuma more abubuwa tare yayin da suke cudanya da juna. Sa'an nan za su ba da gudummowarsu wajen yin mu'amala da koyi da juna a tsakanin mabambantan al'adu, sannan za su zauna tare cikin jituwa, a kokarin sa kaimi kan bunkasuwar dan Adam baki daya. (Tasallah Yuan)