in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da shugabar gwamnatin Jamus
2015-10-29 21:25:33 cri

A yau da safe ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da shugabar gwamnatin kasar Jamus madam Angela Dorothea Merkel a nan Beijing, inda bangarorin 2 suka yaba wa ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen 2, inda suka amince da kara inganta hadin gwiwar a-zo-a-gani a tsakaninsu a sassa daban daban, a kokarin tabbatar da kyakkyawar bunkasuwar huldar abokantaka daga dukkan fannoni da ke tsakanin Sin da Jamus yadda ba tare da tangarda ba.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, bunkasuwar huldar da ke tsakanin Sin da Jamus tana taimakawa wajen raya huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Turai, yayin da ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Turai ke taimakawa wajen bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da Jamus. Kasashen Sin da Turai sun cimma daidaito kan gaggauta yin shawarwari a tsakaninsu a fannin yarjejeniyar zuba jari da dai sauransu, don haka Sin na fatan Jamus za ta taka rawa wajen kara azama kan daukar wadannan matakai. Har wa yau Sin ta yaba wa Jamus da ta goyi baya da shiga cikin shirin nan na"ziri daya da hanya daya" da kafa bankin zuba jari kan ayyukan more rayuwar jama'a na Asiya wato AIIB. Kasar Sin na son inganta hadin gwiwa da Jamus cikin kungiyar G20.

A nata bangaren, madam Merkel ta ce, a sabon halin da ake ciki, Jamus na son zurfafa hadin gwiwa da Sin a fannonin tattalin arziki da ciniki, sana'o'i, da harkokin kudi. Za kuma ta shiga cikin gudanar da shirin "ziri daya da hanya daya" da kafa bankin AIIB cikin himma. Jamus da Sin suna da moriyar bai daya da kuma karfi na yin hadin gwiwa a al'amuran kasa da kasa, za su kara taimakawa juna, a kokarin daidaita batutuwan kasa da kasa da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya da ma duniya baki daya.

A yau da safe ne kuma Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya yi shawarwari da madam Merkel a nan Beijing. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China