Sassa daban daban na Birtaniya suna ganin cewa, ziyarar shugaba Xi a wannan karo za ta sa kaimi ga raya dangantaka tsakanin Sin da Birtaniya a duk fannoni, da bude wani sabon babi na kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare a wannan sabon karni. Ana ganin kamata ya yi kasar Birtaniya ta yi amfani da wannan zarafi, na yin kokarin samun ci gaba tare da kasar Sin. sannan kuma, manufar Sin ta neman samun bunkasuwa cikin lumana za ta jawo bunkasuwa ga duniya baki daya.(Fatima)