in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba zai gaza kaso 6.5 cikin shekaru 5 masu zuwa ba, in ji shugaba Xi
2015-11-03 19:13:46 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce mizanin ci gaban kasarsa ba zai gaza kaso 6.5 cikin shekaru 5 masu zuwa ba, muddin za a kai ga cimma nasarar ribanya ma'aunin GDP, da kuma kudaden shigar da al'ummar kasar ke samu nan da shekarar 2020 bisa hasashen da aka yi a shekarar 2010.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne ga mahalarta cikakken taro na 5, na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, yayin da yake karin haske game da shawarar kafa kudurin ci gaban kasar Sin na 13, wanda za a aiwatar cikin shekaru 5.

Ya ce, domin cimma wannan buri na bunkasa GDP, da yaukaka kudaden da 'yan kasa ke samu a kauyuka da birane, ya zama wajibi Sin ta wanzar da matsakaicin ci gaba cikin shekaru 5 masu zuwa.

Kaza lika shugaban na Sin ya ce, wanzuwar matsakaicin ci gaba za ta bunkasa yanayin zamantakewar al'umma, ta yadda za su iya cin gajiyar nasarorin kasarsu, tare kuma da dawwamar managarcin ci gaba tsakankanin al'umma.

Daga nan sai ya yi fatan ci gaban da Sin za ta cimma cikin shekaru 5, baya ga bunkasuwa, zai kuma kunshi nagarta, ya kuma shafi daukacin sassan ci gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China