Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gaya ma shugaban hukumar yankin Taiwan na kasar Sin Ma Ying-Jeou a ranar Asabar din nan lokacin da suka gana da juna cewa, babu abin da zai iya shiga tsakanin bangarori biyu da ke mashigin tekun Taiwan, wato babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan na Sin, saboda su 'yan uwan juna ne.
Tarihin shekaru 66 na zumuncin dake tsakaninsu ya nuna cewa, duk abin da zai faru da bangarorin ke fuskanta kuma komin dadewa da za su yi suna janyewa daga juna, ba za su iya rabuwa ba, in ji Shugaba Xi.
Shugaba Xi Jinping ya kara da cewa, su 'yan uwan juna ne na jini, koda kuwa an karya kashin jikinsu.
Shugaba Xi ya lura da cewa, a wannan rana ga shi suna zaune tare da juna domin hana tabarbarewar tarihi ya sake nanata kanshi, ya kuma kawo ciksa na cigaban zaman lafiya a tsakanin sassan biyu. Hakan kuma zai ba da dama ga shugabannin bangarorin biyu su cigaba da samar da sararin wanzar da zaman lafiya, wanda zai ba da dama ga zuriyoyinsu nan gaba su amfana daga makoma mai kyau.(Fatimah Jibril)