Wannan shi ne ziyarar farko ta shugaba Xi a matsayinsa na shugaban kasar Sin kuma shi ne shugaban kasa na farko da ya isa kasar Singapore tun bayan babban zaben kasar a ranar 11 ga watan Satumba.
A lokacin ziyarar tasa, shugaba Xi Jingping zai gana da takwaransa shugaba Tan Keng Yam da kuma firaministan kasar Lee Hsien Loong a hukumance sannan kuma zai halarci liyafar da shugaba Tan zai shirya masa. (Bilkisu)