in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai kai ziyarar aiki a Singapore da Viet Nam
2015-10-30 21:36:39 cri

A yau Jumma'a 30 ga wata, a yayin taron manema labaru da aka yi, Liu Zhenmin, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin da Li Jun, mai ba da taimako ga shugaban sashen yin cudanya da kasashen waje na kwamitin tsakiya na JKS. sun yi karin bayani kan ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping na kasar zai yi a kasashen Singapore da Viet Nam.

A cewar Liu Zhenmin, a lokacin ziyararsa a Singapore, shugaba Xi da shugabannin Singapore za su yi musayar ra'ayoyi kan huldar da ke tsakanin kasashen 2 da zurfafa hadin gwiwar su a sassa daban daban. Haka kuma za su tsara shiri da manufa kan yadda za a bunkasa huldar dake tsakanin kasashen 2. An yi imani da cewa, wannan ziyara za ta kara daga matsayin dangantaka a tsakanin kasashen 2, inganta amincewar juna a tsakaninsu ta fuskar siaysa, kyautata hadin gwiwarsu ta a-zo-a-gani, tare da kara azama kan ci gaban huldar da ke tsakanin Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN.

Har wa yau, Li Jun ya ce, a lokacin ziyarar sa a Viet Nam, shugaba Xi zai yi shawarwari da shugabannin Viet Nam kan huldar da ke tsakanin kasashen 2 da wasu al'amuran da ke jawo hankalinsu, a kokarin kara inganta amincewar juna ta fuskar siyasa, habaka hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2, tare da tsara manufa kan yadda za a raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 a nan gaba. An yi imani da cewa, sakamakon kokarin da Sin da Viet Nam suke yi tare, ba shakka wannan ziyara za ta samu nasara, wadda kuma za ta sa kaimi kan samun sabon ci gaba mai muhimmanci wajen raya huldar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 daga dukkan fannoni, tare da ba da gudummowa a fannin wanzar da zaman lafiya da wadata a shiyya-shiyya da duk duniya baki daya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China