in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: Sin za ta nace ga hanyar samun bunkasuwa cikin lumana
2015-11-07 13:46:07 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi a Jami'ar kasar Singapore a ranar Asabar din nan 7 ga wata, inda ya jaddada cewa, Sin ta taba fama da hari daga kasashen waje da kuma yakin basasa, abin da ya kawo babbar illa da barazana ga jama'arta. Hakan ya sa, Sinawa suka fahimci mana'ar zaman lafiya sosai, don haka kasar Sin ba za ta yi watsi da tunanin kiyaye zaman lafiya ba, kuma ba za ta sanya sauran kasashe cikin wahala ba ko kadan.

Shugaba Xi ya ce ko shakka babu, Sin za ta samu bunkasuwa mai wadata, amma ba za ta aiwatar da mulkin mallaka ba har abada. Wasu mutanen da ba su fahimci matakan da Sin ke dauka sosai ba, ko wassu da ke da wani mugun nufi da masu bambancin ra'ayi ko rashin fahimta kan kasar Sin, suna jita-jitar cewa, bunkasuwar Sin za kawo barazana ga sauran kasashe.

Mista Xi ya ce, Sin na nacewa ga hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, za ta kuma ci gaba da daukar manufar diplomasiyya ta samun bunkasuwa da dogaro da karfin kanta da shimfidar zaman lafiya, wanda hakan ba mataki na gajeren lokaci ba ne, kuma ya kasance babban tsari da alkawarin da Sin ke dauka.

Yayin da yake tabo maganar tekun Nanhai, Mista Xi ya ce, wadannan tsibirori yankin kasar Sin ne tun asali, don haka kiyaye ikon mulkin kasar da cikakken yankin kasa nauyi ne dake bisa wuyan gwamnatin kasar Sin.

Bugu da kari, Mista Xi ya ce, ana samun kwanciyar hankali a tekun Nanhai, sannan kuma Sin za ta nace ga hanyar yin shawarwari da wasu kasashe dake da nasaba da wannan batu bisa ka'idar mutunta tarihi da dokar kasa da kasa don warware sabanin da ke tsakaninsu. Har ila yau shugaban na kasar Sin Xi Jinping ya kuma bayyana imaninsa da cewa, Sin za ta iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun Nanhai bisa hadin gwiwa da kasashen ASEAN. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China