in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban kasar Sin a Birtaniya ta bude wani sabon babi tsakanin kasashen biyu, in ji ministan harkokin waje na Sin
2015-10-24 13:34:45 cri
Daga ranar 19 zuwa 23 ga wata, shugaban kasar Sin ya kai ziyarar aiki kasar Birtaniya. Bayan kammala ziyarar kuma, ministan harkokin waje na Sin, Wang Yi ya bayyana cewa, wannan ziyara ta tabbatar da sabon matsayin dangantaka tsakanin Sin da Birtaniya, tare da bude wani sabon babi ga kasashen biyu.

A yayin ziyarar, shugaba Xi ya yi shawarwari da firaministan Birtaniya, David Cameron tare da samun daidaito a tsakaninsu, inda bangarorin suka yanke shawarar kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare a duk fannoni a wannan sabon karni, da bude wani babi mai daraja a tsakaninsu. Wang Yi ya ce, kasashen biyu sun yanke wannan shawara ce bisa babbar moriyar kasa cikin dogon lokaci da kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya da wadata a duk fadin duniya.

Wang Yi ya ce, wannan ne karo na farko da shugaba Xi ya kai ziyara a Birtaniya, wanda ya zuba sabon karfi wajen sa kaimi ga raya dangantaka tsakaninsu a duk fannoni, da bude wani sabon babi na kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare a duk fannoni. An sami babbar nasara, tare da samun sakamako mai kyau.

Bayan haka, mista Wang Yi ya ce, a yayin ziyarar, shugaba Xi ya sha bayyana manufofin da matsayin da Sin ke dauka, don mai da martani ga harkokin da kasashen duniya ke mai da hankali a kai.

Ya ce, game da damuwar kasashen duniya kan yanayin da Sin ke ciki a fannin tattalin arziki, shugaba Xi ya jaddada cewa, yanzu tattalin arzikin Sin na bunkasa lami lafiya. Duk da matsalar da kasashen duniya ta fannin bunkasuwar tattalin arzikin, yawan tattalin arziki ya karu da kashi 6.9 cikin dari a kasar Sin daga watan Yuli zuwa na Satumban bana, shi ya sa Sin tana ci gaba da taka rawar a zo a gani wajen ba da jagoranci kan raya tattalin arziki a duniya. Bugu da kari, Sin za ta ci gaba da kokarin sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki, da sa kaimi ga yin kwaskwarima, da kyautata rayuwar jama'a da sauransu, da ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar bude kofa ga kasashen waje domin samun moriyar juna, a kokarin samun ci gaban kasar Sin tare da sauran kasashen duniya baki daya.

Ban da haka, game da tababar da aka nuna wa kasar Sin dangane da hanyar da za ta bi wajen samun bunkasuwa, shugaba Xi ya furta cewa, kome ba zai iya rage niyyar kasar Sin da kwarin gwiwarta wajen bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana ba. Sin ba za ta yi barazana ga sauran kasashen duniya ba, ba za ta kawo illa ga sauran kasashen duniya ba.

A karshe kuma, mista Wang Yi ya bayyana cewa, kalaman shugaba Xi sun bayyana kwarin gwiwar Sin kan makomar tattalin arzikin kasar, haka kuma sun bayyana matsayin da Sin ke kasancewa na bude kofa ga kasashen waje, da hakuri, da kuma daukar alhakin da ke bisa wuyanta, wadanda suka kara fahimtar da kasashen duniya kan kasar Sin .(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China