in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiga-jigan siyasa na Somaliya sun nuna alhini ga Basine da ya rasu cikin harin da aka kai a kasar
2015-07-30 11:12:50 cri
Mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin diplomasiyya da hadin gwiwa da kasashen waje na majalisar dokokin kasar Somaliya Mohamed Omar Dalha ya nuna juyayi matuka game da mutuwar wani jami'in ofishin jakadancin Sin da ke kasar Somaliya cikin harin da aka kai a otel din Jazeera da ke birnin Mogadishu babban birnin kasar.

Jami'in ya ce, yana bakin ciki game da harin da aka kai kwanan baya a otel din na Jazeera wanda ya rutsa da wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje da kasar ciki har da kasar Sin, ya kuma nuna juyayi game da mutuwar wani jami'in diplomasiyya a ofishin jakadancin Sin da ke kasar, tare da nuna alhini ga gwamnatin Sin da jama'arta wadanda ke da dankon zumunci da Somaliya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China