Mr. Qmer ya ce, kasar Somaliya ta nuna godiya sosai ga goyon baya da jama'a da gwamnatin Sin suka ba ta. A matsayin wata babbar kasa a duniya, an sake bude ofishin jakadancin Sin a Somaliya a bara. Wannan ne muhimmin goyon baya da Sin ta baiwa jama'ar Somaliya. Kasar za ta ba da taimako wajen sake zabar wani wurin ofishin jakadancin Sin a Somaliya bisa iyakacin kokarinta, tare da daukar kwararran matakan tabbatar da tsaro a can.
Dadin dadawa, Mr. Qmer ya kara da cewa, ta'addanci ya zama babbar matsalar da kasashen duniya ke fuskanta. Gwamnatin Somaliya za ta ci gaba da hadin gwiwa da sauran kasashen duniya domin yaki da kungiyar Al-shabaab. 'Yan ta'addan suna kai hari ne ba tare da nuna bambanci ba, ba za su mai da hankali kan wadanda suka kashe Sinawa ne ko mutanen Somaliya, musulmai ne ko ba musulmai ba. Amma duk da haka, wannan ba zai yi illa ga dangantakar da ke tsakanin Somaliya da Sin ba, in ji mr. Qmer.(Fatima)