in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Somaliya fiye da dubu 3 aka kwashe daga Kenya tun cikin watan Disamba
2015-08-06 09:37:23 cri
Kimanin 'yan gudun hijirar Somliya fiye da dubu 3 dake kasar Kenya suka koma kasarsu bisa son rai tun cikin watan Disamban da ya gabata, a cewar hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta MDD (HCR).

A ranar Laraba, hukumar ta yi amfani da jiragen sama biyu domin kwashe 'yan gudun hijirar Somaliya 112 da ke sasanin 'yan gudun hijira na Dadaab dake arewacin kasar Kenya zuwa Mogadiscio, babban birnin kasar Somaliya.

Haka kuma a cewar hukumar HCR, kwashe mutane na baya bayan nan, na kasancewa wani sabon babi na kwashe 'yan Somaliya dake bukatar komawa kasarsu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China