Rahotanni daga birnin Addis Ababa na kasar Habasha, na cewa yanzu haka an shiga zangon karshe a aikin ginin layin dogo, wanda kamfanin CREC na kasar Sin ke gudanarwa a birnin.
Kamfanin CREC ya fara aikin gina layin na dogo ne dai a shekarar 2012 a hukunce. Layin dogon da ya zama na farko da aka gina a birnin, an kuma gina shi ne bisa ma'aunan fasahohin gina jiragen kasa na kasar Sin.
Tuni dai jami'an ma'aikatar zirga-zirgar kasar ta Habasha, da mahukuntan birnin na Addis Ababa suka bayyana cewa, hanyar dogon tana da muhimmiyar ma'ana ga birnin, da ma kasar Habasha baki daya. Mahukuntan sun yi imani cewa, bisa kokarin hadin gwiwar gwamnatin Habasha, da kamfanin na kasar Sin, da ma na jama'ar Habasha, za a iya fara amfani da layin dogon a farkon shekara mai zuwa. Matakin da zai rage cunkoson ababen hawa a birnin na Addis Ababa. (Danladi)