Mataimakin minista mai kula da harkokin jami'ai da hukumomi na JKS Wang Ercheng, ya shugabanci tawagar sada zumunta ta JKS, a ziyarar aiki da tawagar ke yi a kasar Habasha, tun daga ranar 16 zuwa 19 ga watan nan na Fabarairu.
Yayin ziyarar jagorancin tawagar ya gana da mataimakin shugaban Jam'iyyar EPRDF, da mataimakin firaministan kasar ta Habasha Demeke Mekonnen, da mataimakin shugaban kwamitin kungiyar AU Erastus Mwencha.
Haka zalika, Mr. Wang da 'yan tawagarsa sun halarci taron kara wa juna sani na 'yan Jam'iyyar EPRDF, da kwararru, da manema labaru na kasar Habasha, inda tawagar ta gabatar da bayanai don gane da cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiyar JKS karo na 18, tare da yin musanyar ra'ayoyi kan yadda za a inganta dangantakar abokantaka, tsakanin jam'iyyun biyu, da kasashensu, da kuma dangantakar Sin da nahiyar Afirka da dai sauran muhimman batutuwa.(Danladi)