Da yake hira da 'yan jarida na kafofin yada labarai daban daban, shugaba Mulatu ya bayyana cewa kasar Habasha da kasar Sin suna amfana da kyakyawar dangantaka dake dogaro da yarda da juna, fahimtar juna da kuma girmama juna.
Cigaban dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta biyo bayan wani dogon tarihi har ma da cigaban huldar diplomasiyya data taso tun daga shekarar 1970, in ji shugaban tare da jaddada cewa wannan abokantaka daga dukkan fannoni tana amfana wa kasashen biyu musamman ma ta fuskar siyasa, tattalin arziki da al'umma.
Tare da samun cigaba bisa dogaro da kansu, kasashen Habasha da Sin na kara karfafa dangantakarsu ta hanyar musanyar siyasa, al'adu da ilimi har da taimakawa juna da kwararru in ji shugaba Mulatu Teshome. (Maman Ada)