Babban taron MDD ya kira wani taro don tunawa da cika shekaru 70 da fara aiki da tsarin dokokin majalisar, kuma an zartas da sanarwar cika shekaru 70 da kafuwar MDD.
Mista Liu ya kara da cewa, idan an waiwayi wadannan shekaru 70 da suka gabata, kasancewarta wata hukumar da ke kunshe da bangarori daban-daban, matsayin MDD sai dinga inganta ta yi. Sin kuma, a matsayin kasa ta farko da ta sa hannu kan tsarin dokokin MDD, tana fatan kara hadin gwiwa da mambobin majalisar domin ci gaba da nacewa ga muradu da ka'idojin tsarin, tare kuma da tabbatar da matsaya daya da aka cimma a tarurukan koli na majalisar da aka gudana a kwanan baya ba da dadewa ba, da sa kaimi ga majalisar da ta kyautata ayyukanta, da kuma kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa bisa jigon hadin gwiwar samun moriyar juna, ta yadda za ta cimma muradi da tafarki mai kyau da aka tsara cikin tsarin dokokin majalisar. (Amina)