in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana goyon bayan MDD kan aikin kiyaye zaman lafiya
2015-09-29 19:47:51 cri
A yayin dake halartar taron kolin cika shekaru 70 da kafuwar MDD, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da manyan matakan da kasar Sin za ta dauka wajen goyon bayan ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ke gudanarwa.

Dangane hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Talata cewa, wannan muhimman nauyin ne da kasar Sin ta dauka wajen kiyaye zaman lafiya da tabbatar da tsaro a kasashen duniya,wannan mataki ne da ke nuna aniyar kasar Sin na tabbatar da zaman lafiya a duniya, ya kuma nuna yadda kasar Sin ke goyon bayan MDD.

Daga bisani kuma, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da bangarori daban daban, da goyon bayan ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, ta yadda kasar Sin za ta ba da karin gudummawa ga ayyukan kiyaye zaman lafiya da tabbatar da tsaro a kasashen duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China