Cikin jawabinsa a yayin bikin, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, ma'anar yunwa ba kawai tana nufin karancin abinci ba, har ma, tana nufin rashin adalci, ya kamata a sa kaimi ga kasa da kasa da su hada kai kan aikin kawar da yunwa.
Babban taken ranar na bana shi ne, "kiyaye zaman takewar al'umma da aikin noma, a kawar da talaucin da kauyukan dake fama da shi". Babban sakataren hukumar FAO Jose Graziano da Silva ya ba da jawabi cewa, ana yabawa matuka ga manoman kasa da kasa da dai sauran mutanen da suka ba da babbar gudumawa wajen kyautata abubuwa masu gina jiki na al'ummomin kasashen duniya. Amma, a halin yanzu, mutane kimanin miliyan dari takwas na fama da karancin abincin gina jiki, shi ya sa, ya kamata a samar da karin abinci ga dukkanin al'ummomin kasashen duniya, musamman ma ga wadanda suke fama da karancin abinci, a sa'i daya kuma, a cimma dauwamemmen ci gaba kan ayyukan dake shafar samar da abinci da kuma sayen hatsi. (Maryam)