Zaman lafiya da ci gaba a nahiyar ta Afrika zai zama mafi muhimmanci ga zaman lafiya mai dorewa da ci gaban da kowa zai amfana a duniya, in ji Mr. Liu a taro karo na 70 na majalissar a kan sabon hadin gwiwa don ci gaban Afrika.
Kasashen duniya ya kamata su maida hankali a kan hadin gwiwwa da nahiyar Afrika ta amfani da wata dabara ta musamman tare da kara mai da hankali a ciki da wajen nahiyar kan jadawalin shekara ta 2030 da kuma jadawalin kungiyar tarayyar kasashen Afrikan ta AU na shekara ta 2063 domin a samu babban ci gaba wajen aiwatar da sabon shirin hadin gwiwwa don ci gaban Afrika.
Ya lura da cewa ganin taimakawa ci gaban Afrika yana da matukar muhimmanci ga jadawalin ci gaba mai dorewa na shekara ta 2030, ya kamata kasashen duniya su mai da hankali kwarai a kan bukatun da kalubaloli na musamman su kuma dora muhimmancin wajen warware batutuwa kamar yunwa, talauci, kiwon lafiya wanda yake kawo cikas ga yanayin zaman rayuwa a kasashen nahiyar.
Haka kuma Mr Liu Jieyi ya ce idan aka tabo batun ayyukan ci gaba, ya kamta a bi ka'idar da ya kamata a baiwa nahiyar isashen 'yanci wajen aiwatar da jadawalin shekara ta 2030 tare da ba su tabbacin mutunta ikon kasashen su a cikin ayyukan baki daya. (Fatimah Jibril)