Wakilin kasar Sin na din din din a MDD Liu Jieyi ya bayyana hakan a lokacin taron gaggawa na kwamitin tsaron majalissar a kan wutan dake kara ruruwa tsakanin Isra'ila da Plasdinu.
Ya ce rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu ya kara ruruwa, abin da ke janyo damuwa game da yanayin tsaro a kudancin Kudus, yammacin kogin da ma Gaza. Abin da in ji wakilin Sin yake saka kasar damuwa matuka.
Liu Jieyi ya ce ya kamata kasashen duniya musamman kwamitin tsaron majalissar su mai da hankali sosai a kan bukatar Palasdinu da na kasashen Larabawa. Ta hanyar inganta kokarin bangarorin da abin ya shafa domin samun su tsagaita bude wuta dake wakana a tsakaninsu kuma rage zaman fargaba da ake fuskanta a yankin.
Wakilin dindindin a MDD har ila yau ya ce cimma nasarar samar da zaman lafiya a tsakanin Palasdinu da Isra'ila shi ne hanya mafi dacewa ta warware takaddamar dake tsakanin bangarorin biyu daga nan sai ya bayyana fatan cewar gwamnatin Isra'ila za ta dauki darasi ta hanyar misali mai kyau da kuma bayyana aniya na gari. (Fatimah Jibril)