Wannan jami'i ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping ya halarci tarurukan tunawa da cika shekaru 70 da kafa MDD da taron kula da hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma taron koli na mata a karshen watan Satumba, tare da sanar da wasu matakai a gun wadannan taruruka, wadanda kuma suka shafi fannoni biyar, kamar Sin za ta kafa asusun raya hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, wanda a mataki na farko, za a samar da kudi dala biliyan 2 don nuna goyon baya ga kasashe masu tasowa wajen aiwatar da ajendar samun bunkasuwa bayan shekarar 2015.
Hakazalika kuma, jami'in ya bayyana cewa, ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin da hukumomin da abin ya shafa za su yi nazari tare da daukar matakai bisa bukatun kasashen da za su karbi taimakon, don cika alkawarin Sin na samar da gudummawa yadda ya kamata. (Zainab)