in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da a yi hadin gwiwa domin kawar da talauci da nuna bambanci
2015-10-18 13:55:21 cri
A jiya Asabar 17 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi jawabinsa game da ranar kawar da talauci ta duniya, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su yi hadin gwiwa domin kawar da talauci da nuna bambanci a yayin da suke kokarin tabbatar da shirin samun dauwamammen ci gaba na shekarar 2030.

Ban Ki-moon ya bayyana cewa, a yayin da ake kokarin cimma muradun karni, an sami babban ci gaba a fannin kawar da kangin talauci a duniya. A cikin shekaru 25 da suka wuce, mutane sama da biliyan daya sun fita daga talauci, amma ba kowa ba ne ya ci wannan buri ba. Har yanzu mutane sama da miliyan 900 suna ci gaba da fama da talauci, har ma karin mutane za su iya fada cikin kangin talauci. Sauyin yanayi, ko rikice-rikice, ko sauran nau'o'in bala'u, kowanensu za su iya lalata sakamakon da aka samu a wannan fanni.

Ban Ki-moon ya nuna cewa, shugabannin kasa da kasa sun zartas da shirin samun dauwamammen ci gaba na shekarar 2030, inda suka yi alkawarin kawar da kowane irin talauci kafin lokacin da aka tsai da. Domin mai da martani ga wannan alkawari, dole ne a kawar da kowane irin ra'ayin na nuna bambanci.

A ranar 22 ga watan Disamba na shekarar 1992, babban taron MDD karo na 47 ya yanke shawarar kebe ranar 17 ga watan Oktoba na kowace shekara a matsayin ranar kawar da talauci ta duniya, a wani kokari na jawo hankulan kasa da kasa kan matsalar talauci, domin sa kaimi ga aikin kawar da talauci a duniya baki daya, da sa kaimi ga kasashen duniya da su dauki hakikanin matakai domin ba da taimako ga masu fama da talauci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China