Daraktan UNCTAD mai kula da kasashen Afrika masu tasowa Tesfachew Taffere, ya furta hakan a hirarsa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, ya ce kasar Sin ta giggina muhimman ababan more rayuwa a kasashe masu tasaowa musamman a fannonin makamashi da sufuri.
Ya ce samar da ababan more rayuwar zasu taimaka wajen habaka cigaban tattalin arziki da kasuwanci a kasashen masu tasowa.
Mista Tesfachew, ya yabawa kasar Sin wajen tallafawa kasashen duniya da dama wajen yakar talauci da samar da ayyukan yi ga miliyoyin al'umma.
Idan za'a iya tunawa, a yayin gudanar da babban taron MDD kan batun cigaban kasashen duniya wanda aka gudanar a watan jiya a birnin New York, shugaba Xi Jimping na kasar Sin, ya yi alkawarin bada tallafin kudi kimanin dalar Amurka biliyan biyu domin aiwatar da shirin raya cigaban kasashe masu tasowa nan da shekara ta 2030. (Ahmad Fagam)