Rundunar sojojin kasar Kamaru ta gamu da harin da aka kai mata a yayin da suke sintiri a yankin arewacin kasar dake iyaka da Najeriya, harin da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram da kaiwa, lamarin da kuma ya yi sanadiyyar mutuwar wani jami'in sojan Kamaru, yayin da wasu sojoji 3 suka ji raunuka.
Hedkwatar sojojin kasar ta ba da labarin cewa, an kai hari ne a garin Limani da kasar Kamaru ta mai da shi wani fagen daga na yaki da kungiyar Boko Haram ta kasar Najeriya. (Amina)