A jawabinsa yayin da ya halarci bikin kammala aikin, ministan harkokin albarkatun ruwa da makamashi na kasar Kamaru Bashir ya bayyana cewa, raya makamashi shi ne muhimmancin tushen raya kasar Kamaru.
Ya kuma bayyana cewa, kasashen Sin da Kamaru suna da kyakkyawar makoma wajen yin hadin gwiwa a fannin makamashi, kana ya nuna godiya ga kamfanin Huawei bisa ga jarin da ya zuba a bangaren makamashin da za a iya sake yin amfani da shi, baya ga aikin gina tashar.
Manajan kamfanin Huawei dake kasar Kamaru Ni Zheng ya bayyana cewa, sakamakon karancin wutar lantarki da ake fama da shi a kasar Kamaru, hasken rana ya kasance muhimmin makamashi da zai taimaka wajen samun bunkasuwa mai dorewa a kasar Kamaru a nan gaba. (Zainab)