Mr. Hollande da yake jawabi jim kadan bayan ganawa da shugaban kasar ta Kamaru Paul Biya yace kwanan nan shugaban kasar Nigeriya zai kawo ziyarar aiki a Kamaru don haka yana da matukar muhimmanci ga kasashen biyu sun samu dangantakar zumunci mai kyau.
Shugaban na Faransa dai ya isa Kamaru ne Jumma'an nan da rana bayan da ya ziyarci kasashen Benin da Angola. Wannan ne karo na farko da wani shugaban kasar Faransa ya ziyarci Kamaru cikin shekaru 14 tun bayan da tsohon shugaban kasar na Faransa Jacques Chirac ya je lokacin babban taron Faransa da Afrika a shekara ta 2001.
Shugaban kasar Kamaru a nashi bayanin yace batun yaki da kungiyar boko haram shi ne a kan gaba a ganawar da yayi da shugaban kasar ta Faransa Francois Hollande.