Wani jami'in sojan kasar ta Kamaru ya bayyanawa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, boma-boman sun tashi ne a babbar kasuwar Maroua da karfe 2 da rabi na yammacin wannan rana, kuma kasuwar na daya daga cikin wuraren da jama'a ke taruwa a birnin na Maroua.
Ana dai zargin mayakan kungiyar Boko Haram da kaddamar da wannan hari.
A daya hannun kuma yawan mutanen da suka mutu a sakamakon fashewar boma-boman zai iya karuwa, duba da yawan mutanen da suka samu munanan raunuka a yayin aukuwar wannan lamari. (Zainab)