A cewar wani jami'in rundunar sojin kasar da ya bukaci a boye sunan sa, maharan sun tsallaka zuwa kasar Kamaru ne ta kan iyakar Najeriya da sanyin safiyar Litinin din nan, inda kuma suka aukawa sansanin na 'yan sanda. Ya ce sun kone wasu motoci guda biyu, sa'an nan sun hallaka mutane biyu da ake tsare da shi a ginin na 'yan sanda.
Kaza lika jami'in rundunar sojin ya ce bayan aukuwar lamarin, wasu sojoji 4 da 'yan sanda 3 sun yi batan dabo, ko da yake dai ba a tabbatar da ko maharan ne suka yi awon gaba da su ba.
An ce maharan sun tsare bayan farmakin da suka kaddamar, kafin jami'an tsaro su isa wurin domin daukar wani mataki.