Hakazalika shugaba Biya ya yaba da manyan nasarori da kasar Sin ta samu lokacin da ta fara aiwatar da manufar bude kofa da yin kwaskwarima, kuma ya yaba da dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, jakada Wei Wenhua ya bayyana cewa, kasashen Sin da Kamaru na sada zumunta tsakaninsu, sannan suna hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki, cinikayya, al'adu da sauransu tun bayan da suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu.
Kuma kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Kamaru wajen kara yin mu'amala a tsakanin al'ummomin kasashen biyu, da zurfafa hadin gwiwar don inganta dangantakar da ke tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)