Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi wanda ya ke ziyarar aiki a kasar, a ranar talata 13 ga wata a birnin Yaoundé,.
A yayin ganawar, shugaba Biya ya nuna cewa, Sin ta zama abin koyi ga bunkasuwar duniya, kuma Sin da Kamaru na kokarin kiyaye dangantakar dake tsakaninsu na sada zumunci da hada kai, kuma suna samun ci gaba mai armashi a fannoni tattalin arziki, al'umma, kimiyya da sauransu.
Daga nan sai yayi alkawarin cewa kasar Kamaru za ta ci gaba da karfafa hadin kai tsakanin su nan gaba.
A nashi bangare, minista Wang Yi ya bayyana cewa, Sin na dora babban muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma tana fatan kara amincewa da juna a fannin siyasa, da hadin gwiwa da kawo moriyar juna bisa bukatun kasashen biyu, har ma da sa kaimi wajen karfafa hadin kai tsakanin su ta yadda za su samu bunkasuwa tare.
Ban da haka kuma, Wang Yi ya gana da firaministan kasar ta Kamaru Philemon Yang da takwaransa na kasar Pierre Moukoko Mbonjo. (Amina)