Gaba daya tsawonta za ta kai kilomita 195, wanda take tashi Yaounde, babban birnin kasar zuwa Douala, hedkwatar tattalin arzikin kasar, a yayin da fadin hanyar zai taimaka wajen tafiyar motoci shida, matakin farko dai na fara gina wannan hanya shi ne kammala kilomita 60, kuma adadin kudin za'a kashe a matakin farko ya kai dallar Amurka miliyan 568 bisa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bangarorin biyu.
A karshen watan da ya gabata, lokacin da ministan gine-ginen kasar Kamaru ya kai ziyarar aiki a wurin gine-gine, ya nuna yabo sosai kan yadda kamfanin Sin ke gudanar da aikinsa, bisa kwarewa da kuma saurinsa wajen gudanar da aiki. Haka kuma ya bayyana farin ciki sosai bisa sakamako mai gamsuwa da aka samu cikin watanni biyu da suka gabata.
Manyan dake kula da wannan aiki, Du Siyong ya bayyana a ran 4 ga wata cewa, za a iya kammala aikin matakin farko a karshen shekarar 2018, idan kome na gudana yadda ya kamata.
Lamarin da kuma zai ci gaba da taimakawa wajen samar da karin guraben aikin yi ga mazauna wurin da aikin gina babbar hanyar ya shafa. (Maryam)