Sanarwar ta bayyana cewa, Ban Ki-moon ya yi tir da harin da aka kai a garin Fotokol dake yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru a ranar 12 ga wata, baya ga nuna yabo ga matakan yaki da kungiyar Boko Haram da wamnatin kasar Kamaru ta dauka. Kana Ban Ki-moon ya kalubalanci kasar Kamaru da sauran kasashe dake yankin da su ci gaba da yin hadin gwiwa don tinkarar barazanar da kungiyar Boko Haram ta haifar musu.
A ranar Lahadi ne wata mace da aka zaton 'yar kungiyar Boko Haram ce ta tayar da bam din da ke jikinta a tsakiyar garin Fotokol dake yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru, inda nan take ta mutu, kana mutane 13 ciki har da wani sojin kasar Chadi su ma suka rasa rayukansu sanadiyar harin. (Zainab)