Wang Yi ya bayyana cewa, kwalejin Confucius na tamkar wata gadar dake sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka.
Haka kuma, Wang Yi ya kara da cewa, kamata ya yi Sin ta ci gaba da yin kokari, ta yadda matasa a kasar Kamaru zasu yi imanin cewa, kasar Sin wata babbar kasa ce dake daukar alhakin kanta da sada zumunta da yin kokarin samun bunkasuwa tare da abokanta na Afirka. Don haka, ya kamata kowane mutum ya zama mai goyon baya da sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka, da kuma yin kokari tare a wannan fanni. (Zainab)