Mr Harris wanda ya fadi hakan, a yayin taron kara-wa-juna-sani game da tattalin arzikin duniya na tsakiyar shekarar 2015, da aka yi a jiya Talata 23 ga wata a birnin New York, ya ce, akwai alama cewa, an samu tafiyar hawainiya wajen raya tattalin arzikin Sin, kuma wasu ma'aunin tattalin arziki bai kai yadda ake hasashe ba, amma idan aka yi la'akarin da wasu matakan sa kaimi ga tattalin arziki da aka dauka, tattalin arzikin Sin zai karu da kashi 7 cikin 100 a karshen rabin shekarar bana.
Ethan Harris ya ce, yanzu, Sin ta kama hanya yadda ya kamata don yin gyare-gyare wanda kuma aka riga aka yi za su warware wasu muhimman matsalolin da suka shafi tattalin arziki, sannan zai kyautata ingancin kasuwanni, da inganta bin doka, da kara yin amfani da kasuwanni don kyautata albarkatun kasar.(Bako)