in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon firaministan Faransa ya musanta ra'ayoyin kasashen yammacin duniya dangane da raguwar tattalin arzikin Sin
2015-09-08 14:05:28 cri
Tsohon firaministan kasar Faransa Jean-Pierre Raffarin ya bayyana a birnin Paris cewa, a 'yan kwanakin nan, wasu kasashen yammacin duniya ba su bayyana hakikanin yanayin tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata ba.

A yayin taron shugabannin kamfanonin Sin da Turai karo na 6 da aka yi a birnin Paris na kasar Faransa, Raffarin ya ce, wasu kasashen yammacin duniya su kan yin nazari kan tattalin arzikin kasar Sin ne bisa wasu kananan bayanai da suka samu, inda suke ganin cewa, sakamakon da suka fidda na shafar dukkanin fannonin tattalin arzikin kasar Sin. lamarin da ya sa, ba su fahimci tushen tattalin arzikin kasar ta Sin ba, watau harkokin dake shafar jama'a da sha'anin kudin kasar.

Don haka a ganin sa, shugabannin kasar Sin suna kula da batun karuwa da kuma yin kwaskwarima ga tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.

Kaza lika, Mr. Raffarin ya ce, yadda tattalin arzikin duniya ke farfadowa bai kai hasashen da aka yi ba, ci gaban tattalin arzikin wasu kasashen na tangal-tangal.

Wannan ya sa, kasar Sin ta mayar da hankali ga kare muradunta tare da bunkasuwar yankin, matakin da ya sa kasar Sin ta samar da babban gudummawa wajen warware matsalolin kasa da kasa da shiyya-shiyya.

Bugu da kari, ya ce, shirin nan na zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, kafuwar sabon bankin raya kasashen BRICS da wasu shirye-shirye da kasar Sin ta bullo da su suna da ma'ana wajen ciyar da bunkasuwar mu cikin hadin gwiwa gaba, kana za su taimaka wa bunkasuwar kasashen Asiya, da samar da kyawawan damammaki ga kamfanonin kasashen Turai. A sa'i daya kuma, wata dama ce ta hadin gwiwa ga kamfanonin kasashen Sin da Turai da za su yi a kasuwannin Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China