Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fada a yau Litinin cewar, bisa binciken da aka yi, an gyara karuwar tattalin arzikin kasar a shekarar 2014 zuwa kashi 7.3 cikin 100.
Wata sanarwa daga hukumar ta nuna cewar, ma'aunin tattalin arzikin GDP na kasar a bara ya tasamma yuan trillion 64.61, kwatankwacin dalar Amurka trillion 10, sai dai a bisa alkaluman kididdigar adadin ya ragu da yuan biliyan 32.4, lamarin da a cewar hukumar kididdigar kasar ya dora ma'aunin tattalin arzikin kasar a kashi 7 da digo 4 a halin yanzu.(Ahmad Fagam)