Kakakin hukumar Sheng Laiyun wanda ya bayyana hakan cikin shafin hukumar a yaur Litinin, ya kara da cewa, ci gaban da aka samu sun faru ne sakamakon manufofi da matakan yin gyare-gyare da gwamnati ke aiwatarwa.
Sheng ya ce, bangarorin da aka samu wannan ci gaba sun hada da bangaren masana'antu, zuba jari da kuma ribar da aka samu a sashen kayayyakin bukatu na yau da kullum.
Ko da yake Mr. Sheng ya yi gargadin cewa, duk da wannan ci gaban da aka samu, kamata ya yi gwamnati da kara sa-ido kan irin matsalolin da za su iya kunno kai, sannan a shirya daukar kwararan matakai don cimma ci gaban da ake fata na kashi 7 cikin 100 a wannan shekara. (Ibrahim)