in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai ziyarci gidan firaministan kasar Birtaniya
2015-10-14 11:15:22 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasar Birtaniya daga ran 19 zuwa 23 ga wannan wata, yayin ziyararsa, Mista Xi zai ziyarci gidan firaministan kasar David Cameron na Chequers a garinsa, inda bangarorin biyu za su gana da juna.

An ba da labari cewa, Birtaniya ta dora babban muhimmanci kan ziyarar Mista Xi a wannan karo, za ta kuma yi maraba da Mista Xi bisa babban mataki. A cikin ziyararsa na tsawo kwanaki 4, Mista Xi zai gana da sarauniya Elisabeth na biyu a fadar Bukingham, sannan zai gana da firaministan kasar David Cameron a ofishinsa a titin Downing. Daga baya kuma, Mista Xi zai kai ziyara a gidansa na Chequers dake karkarar garinsa, abin da zai jawo hankalin mutane. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China