Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani inda suka amince da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashensu, bayan kammala cimma matsaya kan batun shirin nukiliyar kasar ta Iran.
Shugaba Xi, ya ce, Iran za ta samu damammakin na kulla zumunci da kasashen duniya da dama idan har ta amince da aiwatar da shirinta na nukiliya, sannan dangantakar Iran da kasar Sin za ta sake samun tagomashi.
Ya kara da cewar, kasar Sin tana ba da muhimmanci ga dangantakar dake tsakaninta da Iran, kuma kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar huldar diplomasiyya ne tun shekaru sama da 40 da suka shude.
A nasa bangaren, Rouhani, ya ce, Iran tana martaba dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma a halin da ake ciki yanzu tana sake yin nazari ne kan sabbin hanyoyin da za su tabbatar da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, musamman a bangarorin tattalin arziki da kasuwanci da makamashi.(Ahmad Fagam)