in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Nijeriya
2015-09-28 08:59:00 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari a jiya Lahadi a birnin New York.

Yayin ganawarsu, Shugaba Xi, ya jaddada cewar, kasashen Sin da Najeriya na da dankon zumunci a tsakaninsu, kuma dangantakar ta shafi muhimman tsare-tsare ne na hadin gwiwa don cin moriyar juna da kawo maslaha ga jama'ar kasashen biyu, kuma akwai bukatar kasashen biyu su bi alkiblar da zata tabbatar da zumunci dake wanzuwa tsakanin kasashen biyu ya dore, musamman wajen ba da fifiko ga sha'anin tattalin arziki na kasashen biyu.

Mr. Xi ya ce, shekara mai zuwa ce dangantakar diplomasiyya dake tsakanin kasashen Sin da Nijeriya ta cika shekaru 45 cif da kulluwa, shugaban ya ce kasar Sin tana fatan inganta hadin gwiwa a fannin tsaro da tabbatar da mu'amala daga duk fannoni a tsakaninsu, don tabbatar da cin moriyar kasar Sin da kasashen Afika da sauran kasashe masu tasowa na duniya.

Xi ya kara da cewar, bana shekaru 15 ke nan da kafa dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, za a yi taron tattaunawa karo na 6 tsakanin ministoci na kasar Sin da kasashen Afrika. Kasar Sin ta yi na'am da shawarar da bangaren Afrika ya gabatar na daga matsayin taron zuwa taron kolin bangarorin biyu, kuma tana fatan yin kokari tare da kasashen Afrika, don kafa dandali har ya zamanto taron inganta hadin gwiwa da raya makomar dangantaka a tsakaninsu.

A nasa bangare, shuagaba Buhari na Najeriya, ya jinjinawa irin taimako da Sin ta baiwa Najeriya cikin dogon lokaci wajen harkokin tsaro da raya tattalin arziki, sannan yace hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu wajen samar da ababen more rayuwa da aikin gona, da raya harkokin ruwa da samar da lantarki sun kasance wasu manyan ginshikai na raya dangantakar kasashen biyu.

Shugaba Buhari ya ce Najeriya za ta dukufa ka'in da na'in wajen raya dangantakar dake tsakanin ta da Sin a dukkan fannoni. Sannan ya yabawa shugaban Xi sakamakon shirya taron kolin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wanda za a yi a bana a Afrika ta Kudu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China