Shugaban kasar Sin Xin Jinping wanda ke ziyara a halin yanzu, a ranar Lahadin nan ya gabatar da kyauta ta musamman ga kwamitin MDD a birnin New York domin jaddada goyon bayan al'ummar Sinawa ga kwamitin na MDD.
Yayin bikin tunawa da cika shekaru 70 da kafa kwamitin na MDD, kasar Sin, ta yanke shawarar gabatar da kyautar ne mai taken "Zun of peace" wato kyautar zaman lafiya, kuma wannan wata dadaddiyar al'ada ce ta kasar Sin,sannan bikin mika kyautar, ya samu halartar babban sakataren MDD Ban Ki-moon.
Mista Xi, ya bayyana cewar, wanann kyauta ta musamman, tamkar yin mubaya'a ne ga ayyukan kwaiatin MDD daga al'ummar kasar da adadin su ya kai biliyan 1 da milyan 300.
Shugaba Xi, ya kara da cewar, wannan kyauta ba ta tsaya ga nuna irin dadaddiyar al'adar Sinawa da ci gaban da suka samu ta fuskar wayewa ba, har ma da irin yadda kasar ta samu ci gaba a zamanance, musamman ta hanyar shiga a dama da ita a harkokin duniya.
Wannan kyauta ta "Zun of Peace" ta bayyana karara yadda kasar Sin ke ba da muhimmanci kan batutuwa da suka shafi zaman lafiya da ci gaba da hadin kai da kuma cin moriyar juna wanda su ne kashin bayan kudurorin MDD.
A yayin da MDD ke kokarin bude wani sabon shafi na ci gaba, shugaba Xi ya ce, kasar Sin a shirye take ta goyi bayan MDD domin ganin haka ta cimma ruwa.
A nasa bangare, babban sakatare Ban Ki-moon ya yaba wa gwamnatin kasar Sin saboda kyautar da ta bai wa MDD.(Ahmad Fagam)