Kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Mista Shen Danyang ya bayyana yau cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai kasar Burtaniya a kwanaki masu zuwa za ta kara haskaka dangantaka da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu daga dukkanin fannoni, tare da samar da wata dama mai kyau da za ta bude sabon shafin dangantakar Sin da Birtaniya.
Mista Shen ya kuma ce, Sin da Birtaniya sun hada kai ta fuskar cinikayya yayin da ake fuskantar rikicin basusuka a nahiyar Turai da kalubalen farfadowar tattalin arziki sakamakon rikicin hada-hadar kudi na duniya, ban da haka kuma, kasashen biyu na samun ci gaba yadda ya kamata a fannin ciniki da zuba jari, abin da ya nuna cewa, matakan da Sin da Birtaniya ke dauka a wannan fanni na haifar da moriyar juna, kuma za su samu karin ci gaba mai dorewa a nan gaba. (Amina)