Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar sun halarci bikin tunawa da 'yan mazan jiya a ranar Laraban nan a filin Tian'anmen dake birnin Beijing, inda suka tuna tare da karrama wadanda suka sadaukar da rayuwa.
Wasu sojojin da suka ritaya da iyalan wasu mazan jiya da wakilai daga sassa daban daban sun hallara a filin domin bikin kasar karo na biyu na tunawa da 'yan mazan jiya a jajibarin ranar kafuwar kasar ta ranar 1 ga watan Oktoba.
Yan mazan jiyan kamar yadda gwamnati ta kira su, mutane ne da suka sadaukar da rayuwansu domin samar da 'yancin kasar da ci gabanta, har ma da walwalar al'umma na zamanin yanzu, ko kuma bayan yakin Opium na farko wato tsakanin shekara ta 1840-1842, an ce, Sin tana da wadannan mutane miliyan 20.
Majalissar wakilan kasar Sin ta amince da ranar 30 ga watan Satumbar bara ta zama ranar tunawa da 'yan mazan jiya.(Fatimah)