A jiya ne mambobin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin suka yi taro karo na 27 domin nazartar salo da tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa.
A yayin wannan zama, babban sakataren JKS Xi Jinping ya jaddada cewa, babban makasudin kasar Sin na shiga ayyukan tafiyar da harkokin kasa da kasa shi ne, a yi kokarin raya kasar Sin mai zaman wadata ya zuwa shekarar 2021 da raya kasar Sin ta zamani bisa tsarin gurguzu ya zuwa shekarar 2049, da kuma cimma burin da kasar ta sanya a gaba na inganta rayuwar al'ummarta.
Don haka ya zama dole a yi la'akari da halin da ake ciki da yadda lokaci ke tafiya, a kuma yi amfani da damar samu, a daidaita kalubale yadda ya kamata, sa'an nan a daidaita harkokin cikin gida da na waje tare, a yi kokarin kyautata tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa bisa doka da adalci, ta yadda za a kara samar da sharadi mai kyau wajen bunkasa kasar Sin tare da samar da zaman lafiya a duniya. (Tasallah Yuan)