Sakatare janar na M.D.D. Ban Ki-Moon ne ya shugabanci taron, yayin da shugaban kasar Peru Ollanta Moisés Humala Tasso dake shugabancin karba-karbar na taron kan sauyin yanayi na shekarar 2014 da takwaransa na Faransa François Hollande, wanda ke shugabancin taron na shekarar 2015, da shugabannin kasashen Masar, Brazil, Amurka da Nijeriya da sauran shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 30 sun halarci taron.
Shugaba Xi ya ce, taron Paris game da sauyin yanayi da za a yi a karshen shekarar bana, zai tsara sabon shirin game da matsalar sauyin yanayi a duniya, zai kuma bullo da hanyar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. Ana fatan taron Paris zai daddale yarjejeniya don daukar hakikanin matakan warware wannan matsala. Ya zama dole a bi ka'idoji wajen daddale yarjejeniyar, da bin ka'idar daukar alhakin tare, tare da la'akari da bambancin dake tsakani, Ya zama wajibi kasashen duniya su ba da nasu gudummawa don magance matsalar sauyin yanayi bisa yanayin da ake ciki a kasashensu. Ya zama wajibi kasashe masu wadata su sauke nauyin dake wuyansu wajen ba da kudade da fasahohi, don cika alkawarin da suka dauka na samar da kudaden da yawansa ya kai dalar Amurk biliyan 100 a ko wace shekara, da samar da fasahohi ga kasashe masu tasowa.
Xi ya jaddada cewa, Sin na sauke nauyin dake kanta cikin yakini, kuma ta sanya batun magance matsalar sauyin yanayi cikin babban shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar.
Haka kuma, Sin za ta ingiza amfani da asusun hadin gwiwa da ke tsakanin kasashe masu tasowa, don taimakawa kasashen magance wannan matsala. Ban Ki-Moon ya gode wa shugabannin kasashen duniya sabo da dora muhimmanci game da samun bunkasuwa cikin dogon lokaci,kuma yana fatan taron zai taimakawa taron Paris, da gaggauta shirin shawarwari.(Bako)