A ranar Lahadin nan shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wasu shawarwari 4 da suka shafe yadda za'a bunkasa 'yancin mata a duniya, kuma ya gabatar da kuduroirn ne a yayin da yake jawabi a babban taron MDD.
A yayin jawabin nasa a babban taron na MDD, kan batun da ya shafi 'yancin mata, shugaba Xi, ya jaddada cewar, 'yancin mata batu ne mai matukar muhimmanci domin babu yadda za'a iya samu ci gaba a harkokin duniya ba tare da sanya mata ba, bisa la'akari da irin gagarumar rawar da suke takawa yayin duk wata fafutukar neman 'yancin bil adama a doron duniya
Ya ce, a wannan mashahurin taro na tunawa da kafa gidauniyar MDD shekaru 70 da kuma cika shekaru 20 da gudanar da babban taron MDD kan al'amuran na mata a Beijing, Xi ya ce, ya zama tilas su yi nazari kan hanyoyin da za su sake bunkasa rayuwar mata shekaru masu zuwa nan gaba.
Shawarwari 4 da shugaba Xi ya ambata sun hada da:
Na farko, ya ce, dole ne a mai da hankali kan 'yancin mata ta hanyar ba su damar shiga harkokin ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
Na biyu, wajibi ne a martaba mata da samar da dokokin da za su tabbatar da kare musu hakkin.
Na uku, wajibi ne a kawar da dukkanin nau'o'in karfin tuwon da ake nunawa mata..
Na hudu, a yi kokari tare domin kago wani muhalli mai inganci ga mata, domin su samu ci gaba yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)